Sheikh Yakub Yahya Katsina ne, ke cigaba da jagorantar zaman, inda a yau, aka karanto yadda mahaifiyar Sayyid Abdullahi Rahdi (AS) ta kai ma Sayyida Zainab (SA) shi, da niyar a ba Imam Husaini (AS) shi ya kai shi wajen maƙiya ko sun bashi ruwan da zai sha, saboda kwanaki kusan uku bai ci komai ba.
A lokacin da Imam Husaini (AS) ya kai shi ga maƙiya da nufin su bashi ruwa, yana mai shaida masu cewa “Idan ni nayi maku laifi, to shi wannan yaron laifin mi ya yi maku? ina rokon ku da ku bashi ruwa ya sha” wannan ne ya sanya Umar Bin Sa’ad (LA) ya umarci Harmala (LA) da ya shayar da yaron ruwan kibiya, nan take ya tarbe shi da kibiya mai kai uku.
Wannan harbin da Harmala (LA) ya yi ma Sayyid Abdullahi Rahdi (AS) shi ne dalilin shahadantar da shi, ya koma zuwa ga Allah ba tare da ya sha ko da ɗigon ruwa ba.
لا يوم كيومك يا أبا عبد الله...
Your Comment